Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Gwaggwarmayar Kasar Pakistan Ta Kalubalanci Zargin Yin Batanci


Gulalai Ismail

Wata 'yar gwaggwarmaya ta yi watsi da al'ada tayi wani abin basabonba wajen yin karar mutumin dake zarginta da keta dokar batanci.

An zargi Gulalai Ismail, wadda ta kafa wata kungiya mai zaman kanta a Pakistan da ake kira Yammatan Aware, "Aware Girls", da yiwa addini batanci, zarginda ta musanta.

Hamza Khan, dan shekaru 23,wani dalibi daga lardin Khyber Pakhtunkhwa ya fara wani kamfe ta hanyar sada zumunci a kan Gulalai, yana zarginta da yiwa addini da al'adar Pashtun batanci" Bisa ga dukan alamu baya jin dadin rawar da take takawa a matsayin 'yar gwaggwarmaya.

Khan, wanda yayi ikirarin cewa shine shugaban kungiyar matasa da ake kira "Mardan Youth Parliament", ya dora wani hoton bidiyo na tsawon minti goma sha biyu a shafin sadarwarsa na Facebook ranar 20 ga watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, inda ya yi kira da a kaiwa Gulalai harin taron dangi sabili da laifin batanci. .

Gulalai tayi karar Khan a hukumar binciken laifuka da kasa ranar 21 ga watan Nuwamba sabili da fargaban abinda ka iya faruwa da ita, da ya sa aka kama Khan cikin makon nan bayanda wata kotu a Peshawar ta bada takardar sammacen kama shi.

Hukumomin Pakistan sun dauki mataki, yayinda kamfanin Facebook ya sauke hoton bidiyon da ake jin Khan yana cewa, tilas ne kawar da Gulalai domin kare addinin Islama.

Gulalai ta shaidawa VOA cewa tana so ta zama muryar wadanda aka yiwa kage.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG