Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Wasa Serena Williams Ta Lashe Gasar Wimbledon Karo Na 7


'Yar Wasan Kwallon Tennis Ba'amurkiya Serena Williams, Lokacin Murnarta Na Lashe Gasar Wimbledon, July 9, 2016.
'Yar Wasan Kwallon Tennis Ba'amurkiya Serena Williams, Lokacin Murnarta Na Lashe Gasar Wimbledon, July 9, 2016.

Shahararriyar Ba’amurkiyar nan ‘yan wasan kwallon tanis Serena Williams ta sake lashe gasar wasan tanis din nan na Wimbledon a karo na 7, wacce ta dankwafe mafi yawancin nasarorin da ‘yar wasa Steffi Graf ta Jamus ta samu.

‘Yar wasa Serena da take a matsayin lamba daya a wasan tanis a duniya, ta yi nasara akan Bajamushiya Angelique Kerber da ci 7 da 5 da kuma 6 da 3 a ranar Asabar din data gabata a birnin London.

Serena ‘yar shekaru 34 a duniya ta rasa nasarar wasanni 3 a jere a manyan wasannin da aka yi tun bayan lashe gasar ta Winbledon a shekarar data gabata.

Daya daga cikin wasannin da bata sami nasara ba har da wani da ta sha kashi a hannun ita ‘yar wasa Kerber da aka buga a Australia,

Har yanzu dai Williams tana bukatar cin wasu manyan wasanni guda biyu don share mata fage buga wani babban wasan tanis din da ke kira Australian Margret Court.

XS
SM
MD
LG