Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaida Wuta Da Aka Cimma A Sudan Ta Kudu Bata Yi Tasiri Ba


"Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu
"Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Har yanzu ana zaman tankiya a a Sudan ta Kudu sakamakon rashin tabbas a kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma

Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya mai wanzar da zaman lafiya, ya fada jiya laraba cewa, yarjejeniyar da aka cimma ta dakatar da bude wuta a kasar Sudan ta kudu batayi tasiri ba domin kuwa har yanzu kasar na cikin halin zaman dar-dar.

Har yanzu ana zaman tankiya duk ko da yake an cimma matsaya na dakatar da bude wuta wanda shugaban kasar Salvar Kirr ya amince dashi.

Yanzu haka dai ana ci gaba da fada a wadansu sassan kasar kamar yadda Jean-Pierre Lacriox ya shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Yace musali a arewacin kasar, sojojin gwamnati sun fatattaki sojojin ‘yan adawa daga wurin da suke da karfi a yammacin gabar kogin NILE,

Sai kuma a gabashi sojojin sun karbe garururuwan dake arewacin Jonglei yayinda kuma a yammaci ana samun fada tsakanin sojojin gwamnati da na ‘yan adawa a yankin Wau, sai kuma a kudanci inda yanzu haka mutane duk sun watse a wadansu garuruwan dake yankin Ekutorial, suka zama kango

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG