Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Amurka Ke Mayarda Ofishin Jakadancinta Na Israila Birnin Qudus


Diyar Shugaban Amurka Ivanka Trump da mijinta Jared Kushner da suka isa Israila domn bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus
Diyar Shugaban Amurka Ivanka Trump da mijinta Jared Kushner da suka isa Israila domn bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus

Ivanka Trump diyar shugaban Amurka Donald Trump da mijinta sun isa Israila wurin bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus

Diyar shugaban Amurka Ivanka Trump ita da mijin ta Jared Krushner har sun sauka Israila kafin bikin bude sabon ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus.

Yau littini ne dai za a bude wannan ofishin wanda kuma shine ranar da kasar ta Israila ke bikin samun ‘yanci.

Wannan ofishin dai zai zamo na wucin gadi ne domin ko zai rika gudanar da ayyukan sa ne a karamin ofishin jakadancin dake birni Kudus yayin da za a ci gabada neman wani babban wuri da za a gina ofishin na din-din-din a birni Tel Aviv.

Wannan shawarar da Trump ya yanke ya kawo karshen jani inja ka da aka jima anayi game da manufar Amurka na daukar matsayin ‘yar ba ruwana akan wannan batu da ta jima tana kokarin ganin ta samar da jituwa tsakanin yankunan biyu da suka jima suna kai ruwa rana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG