Accessibility links

Alhamis 28, watau Alhamis ta hudu, a watan Nuwamba, Amerkawa ke bikin yiwa Allah godiya da samun sabuwar kasar Amurka, bikin da a turance ake kira "Thanksgiving."

Alhamis hudu ga watan Nuwamba, Amerkawa ke bikin yiwa Allah godiya da samun sabuwar kasar Amurka. Bikin da a turance ake kira (Thanksgiving).Wannan ranar ta hutu ce a ko ina a Amurka, Amerkawa na shakatawa tare da cin abinchi da gudanar da tarukan tintibar juna da zuwa kantuna tare da iyali domin sayen kayan marmari.

Wannan ranar hutu ta “Thanksgiving” iyalai kan hadu waje guda a gasa “Talo-talo” ana ci sannu a hankali ana shewa da annushuwa.A ran Jajiberen wannan rana, Amerkawa ke shirya yin bulaguro. Anji kungiyar masu safarar motoci ta Amurka na bada kididdigar cewa sama da mutane miliyan 43 ne ke kan hanyarsu ta zuwa ziyarar ‘yanuwa a lokacin wnanan hutu. Sai dai hutun wannan shekarar ya hadu da matsalar rashin kyawun yanayi, da hakan ya janyo cikas wajen shirya bulaguro, domin dusar kankara ta zuba sosai a kan hanyoyin zirga-zirga, wasu hanyoyin ma cike suke da dusar kankara har ba’a iya binsu, hakan ya janyo ala tilas aka soke tashin jiragen sama, wasu kuma aka chanza masu lokutan tashinsu.Amerkawa kan maida hankulansu wajen kallon wasanni da shirya ayyukan sa kai na rarraba kayan abinchi ga masu bukata.

A jajiberen wannan ranar, anji shugaba Barack Obama tare da iyalinsa sun gudanar da al’adar nan ta tattara kayan abinchi domin rabawa ga iyalai masu bukata a babban birnin tarayya na Washington. Shugaban na Amurka ya kuma bi al’adar nan ta yin afuwa ga talo-talo biyu wajen jinkirta yankasu domin kalaci a ranar laraba. Shugaban na Amurka yayi hutunsa ne a Fadar shugaban kasa ta “White House”.

A birnin New York kuma,anga yadda jama’a ke kokarin kakkafa tantunansu domin kare kansu daga anyin safiya a lokacin gudanar da Fareting bikin tuna rabnar hutun “Thanksgiving”. Amma abinda ba’a tantance ba shine ko bana ma za’a harba dirka-dirkan robobin zuwa sama safiyar Alhamis ganin yadda yanayin ke kara rinchabewa.
XS
SM
MD
LG