Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Najeriya

Yau Ce Ranar Yaki Da Kwararowar Hamada Ta Duniya


 Kwararowar Hamada
Kwararowar Hamada

Yau kasashen duniya ke tunawa da ranar da Majalisar Dinkin duniya ta kebe domin yaki da kwararowar hamada.

A wannan ranar akan mayar da hankali kan samar da filaye da kuma yanayin da mutane da dabobi ba zasu rasa abinci ba, duba da yadda duniya gaba daya ta sauya sakamakon sauyin yanayi.

Maudu'in wannan shekarar shi ne, samar da abinci da ciyawa da kuma tufafi ta la'akari da kara amfani da wuraren noma a duniya domin samun wadanan ababen na more rayuwa.

Jamhuriyar Nijar, bata yi kasa a guiwa ba, wajen bin sahun takwarorin ta na duniya wajen tunawa da wannan ranar.

Almustafa Garba, shi ne ministan gandun daji na jamhuriyar Nijer, kuma a lokacin da yake wa 'yan kasar jawabi albarkacin wannan ranar ta yaki da kwararowar hamada a kasar da kashi 2 nata bisa 3 ke fama da wannan matsalar, ya ankarar da 'yan Nijar game da barazanar da duniya ke fuskanta.

Kudancin Afirka na daya daga cikin wuraren da ke fuskantar matsanancin fari a duk fadin duniya, lamarin da ya sa kasar Namibia ta ayyana dokar ta baci saboda yanayin da aka shiga a kasar a shekarar da ta gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG