Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau ce Ranar Yara Ta Amnesty International


Yara
Yara

Amnesty International ta kebe rana ita yau ta kowace shekara soboda jawo hankalin duniya akan irin matsalolin da yara ke fuskanta a kasashen duniya daban daban

A wannan rana da Amnesty International ta kebe saboda yara musamman wadanda suka tagayyara ko yaki ko rikici ya daidaita Muryar Amurka ta ci karo da wani dan yaro a sansanin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Muryar Amurka ta zanta da yaron mai suna Wada a sansanin 'yan gudun hijira dake Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

Wada yace garinsu Gwozah kuma suna zaune ne a GRA. Yaron ya ce gudun hijira ya kawoshi Abuja saboda 'yan Boko Haram sun koresu. Idan ba'a manta ba garin Gwozah ya sha samun hare hare daga 'yan Boko Haram. Daga bisani sun kwace garin sun kashe sarkin garin kana suka kafa hedkwatarsu a wurin tare da kafa tutarsu.

Yanzu dai Wada yana makaranta inda ya san abc da kidaya da turanci har zuwa goma. Ya gayawa Muryar Amurka cewa ya koyi komi a makaranta.

Abun mamaki Wada bai san an yi zabe a kasar ba har ma da sabon shugaban kasa.

Dangane da abun da yake son shugaban kasa ya yi sai yace "muna son ya gyra garin". Da aka tambayeshi abun da yake nufi sai yace "muna son ya gyara gari mu koma Gwozah mu zauna lafiya"

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG