Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Iraniyawa ke zaben 'yan majalisar dokokin kasar


Mata sun yi layi wurin kada kuri'u a zaben kasar da su keyi yau Jauma'a

A karon farkon tun bayan da aka cimma matsaya kan shirin nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, Iraniyawa suna kada kuri’unsu a zaben ‘yan majalisar dokoki.

Matsayar dai da aka cimma ta taimakawa Iran an dage mata wasu takunkumi da aka kakaba mata, bayan da ta amince ta rage girman shirin ta na mallakar makamashin na nukiliya.

Akalla ‘yan kasar miliyan 55 ne aka yiwa rijista, wadanda kuma ake sa ran za su kada kuri’unsu a zaben majalisar da ‘yan kwanzavative suka mamaye mafi yawana kujeru 290 da kuma mafi yawan kujeru 88 na wasu kwararru da ke majalisar dokokin kasar.

Ita dai Majalisar, ita ke sa ido akan ayyukan shugaban Addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ke yanke shawara kan harkokin wajen kasar ta Iran.

Kwararru a fannin siyasa na yiwa wannan zabe na ‘yan majalisu kallo a matsayin wani zakarin gwajin dafi kan irin kamin ludayin shugaba Hassan Rouhani, wanda zai sake tsayawa takara a shekara mai zuwa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG