Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba A Ke Yin Zabe A Afirka ta Kudu


Archbishop Emeritus Desmond Tutu ya kada tashi kuri'a wurin zabe
Archbishop Emeritus Desmond Tutu ya kada tashi kuri'a wurin zabe

Yau Laraba ‘yan Afrika ta Kudu suke zabe da ake gani zai jijjiga jam’iyar mai mulki da ta dage tana shugabanci a kasar.

Jam’iyar African National Congress ANC ta mamaye harkokin siyasar kasar tunda Nelson Mandela ya kafa jam’iyar a shekarar alib dubu da dari tara da casa’in da hudu, amma karkashin shugabancin Jacob Zuma, cin hanci da rashawa sun dabaibaye jam’iyar. Yayinda ake fama da rashin aikin yi, da kuma rashin damawa da kowa karkashin jagorancinsa.

Binciken ra’ayoyin jama’a na nuni da cewa, jam’iyar Democratic Alliance zata sami galaba a birane da suka hada da Johannesuburg cibiyar tattalin arzikin kasar. Idan jam’iyar ta sami damar shugabanci yanzu, zai iya bude mata kofar kara samun kuri’u a zaben da za a gudanar cikin shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Rumfar kada kuri'u a Afirka ta Kudu yau Aug. 3, 2016
Rumfar kada kuri'u a Afirka ta Kudu yau Aug. 3, 2016

Zaben cike gurbin da aka gudanar ya haifar da tashe tashen hankali tsakanin jam’iyu da kuma kashe kashe tsakanin ‘yan gani kasheni na jam’iyar ANC da wadansu ‘yan takara. Hukumar zabe da kuma jami’an ‘yan sanda sun ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali yau da sage, inda sama da jami’an ‘yan sanda dubu saba’in da biyar suka kare runfunan zabe.

Afrika ta Kudu zata san inda kasar ta nufa yayinda ake kirga kuri’u a kwanaki masu zuwa.

XS
SM
MD
LG