Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaban Amurka Zai Yi Balaguro Zuwa Orlando


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama zai kai ziyarar Orlando, brinin da Omar Mateen ya hallaka mutane 49 kan ya jikata wasu 53, domin yiwa 'yanuwa da iyalan wadanda harbin ya rutsa dasu ta'aziya da kuma karfafa mutanen birnin da ma jihar Florida gaba daya

Yau Alhamis ake sa ran shugaban Amurka Barack Obama zai yi balaguro zuwa birnin Orlando a jihar Florida, domin ya gana da dangi da iyalan wadanda mummunar harbin kan-mai-uwa-da-wabi mafi muni a tarihin Amurka ya rutsa da su, inda zai yi ta'aziyya da bayyana goyon baya ga birnin da ya kadu matuka da wannan mummunar tarzoma.

Fadar White House tace baya ga ganawa da wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin da aka kai kan wurin shakatawar, haka nan shugaban na Amurka zai kuma gana da 'yan kwana-kwana da masu aikin bada agajin gaggawa da suka kai doki wurin da aka kai harin kai tsaye, da kuma likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya da suke jinyar mutanen nan 53 da suka jikkata a harin.

Ahalinda ake ciki kuma, hukumar da take binciken manyan laifuffuka ta Amurka da ake kira FBI tace, matar Omar Mateen wanda ya kashe mutane 49 a Club din, tana da masaniya gameda harin, kuma bata tuntubi jami'an tsaro ba.

Wani jami'in tsaro yace masu taya masu gabatar da kara tabbatar da tuhuma, da ake kira grand jury da turanci, zasu yi nazarin ko za'a tuhumi matar maharin mai suna Noor Sahi Salman.

Ahalinda ake ciki kuma,wakilan majalisar dattijan Amurka 'yan Democrat suna ci gaba da magana a zauren majalisar, matakin da ya dakatar da duk wata harka a majalisar da zummar tilastawa majalisar baki daya ta yi wani abu kan dokar mallakar bindigogi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG