Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Ranar Matan Karkara Ta Duniya


Matan karkara suna bare rogo

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar goma sha biyar ga watan Oktoba a matsayin ranar matan karkara ta duniya. Ranar da ake jawo hankalin al’umma kan kalubalan da matan karkara ke fuskanta.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya bayyana cewa, kulawa da rayuwar mata mazauna yankunan karkara yana da muhimmanci ga nasarar tabbatar da dorewar muradun karni da Majalisar Dinkin Duniya ta sa gaba.

Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko da rahoto daga birnin Kano, Najeriya inda mata mazauna karkara a jihar dake sana’ar noma da sauran sana’oin dogara ga kai ke kokawa, kan rashin kulawa daga hukumomi.

Wata da wakilin namu yayi hira da ita ta bayyana cewa, tana sana’ar kulikuli amma basu samun wadanda zasu sayi mai, tace sabili da haka ta koma sana’ara saida koko kafin yanzu take kiwo. Tace ta shafe sama da shekaru goma tana wannan sana’ar amma bata taba sumun tallafin ko anini daga gwamnati ba.

Wata kuma mai sana’ar noma tace, suna samun tallafi a lokutan baya daga cibiyar tallafawa ayyukan noma ta kasa-NADA, amma yanzu da kungiyar ta daina bada irin wannan tallafin, suna cin gashin kansu ne, abinda yake shafar abinda suke iya nomawa sabili da rashin karfin sayen taki da kuma biyan bukatun sana’ar.

Wata wakiliyar bankin dake tallafawa manoma a Najeriya da wakilin namu yayu hira da ita, tace tilas ne hukumomi su tallafawa manoma masu karamin karfi idan ana so su kai ga dogaro ga kai, su kuma bada gumummuwa ga samar da isasshen abinci a kasa.

Tace akwai hanyoyi da dama da ya kamata a tallafawa manoma da ya hada da samar da iri mai inganci, da dabarun noma na zamani da kuma taimaka masu wajen samar da kasuwannin abinda suke nomawa.

Tun a shekara ta dubu biyu da uku babban bankin Najeriya ya kebe kudi fiye da Naira biliyan dari biyu domin bada rance ga kananan manoma a kasar, amma har yanzu jihohi da dama basu kai ga cin gajiyar kudaden ba.

Ga cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG