Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mutane Da Suka Halaka A Harim Bam A Bauchi Ya Karu....


Motar kwana kwana tana kashe wuta bayan wani harin bom a Najeriya.

Yawan mutane da suka rasa rayukansu a harin bam da aka kai kan wata kasuwa dake barikin sojoji a Bauchi ya haura daga goma zuwa goma sha hudu.

Yawan Mutane Da Suka Halaka A Harim Bam A Bauchi Ya Karu

Yawan mutane da suka halaka a harin Bam da aka kai kan wata kasuwa a a barikin sojoji a Bauchi ya haura daga goma zuwa goma sha hudu,wadda ya hada da mata da yara,a harin kan wata mashaya dake kasuwar a daren jiya.

Kwamishinan 'Yansandan jihar Mohammed Indabawa,yace kwararru kan harkokin Boma Bomai suna kan hanyar zuwa bauchi daga Abuja,domin tantance irin sindaran da aka yi amfani dasu wajen hada makaman.Suna son sanin Bam din hadin gida ne ko daga waje aka shigo da shi.

Ahalin yanzu kuma iyalai da suka rasa 'yan'uwa a harin,suna zuwa asibiti domin tabbatar da gawarwakin wadanda harin ya rutsa da su.

Wani soja da ya bukaci a saka sunansa ya aza laifin harin kan shugabanninsu.Kamar yadda yake cewa tun watanni suka sami wasikar barazanar za'a kawo musu irin wan nan hari,amma babu wani mataki da aka dauka domin hana aukuwar haka.

XS
SM
MD
LG