Accessibility links

Shuwagabanin kasashen duniya sun sauka a birnin Abuja dake Najeriya domin halartar taron tattalin arziki na duniya.

Indan ka cire ma’aikatan da aikin su ya zama wajibi birnin Abuja tsit yake don hutun da aka bayar sakamakon taron tattalin arzikin duniya a Najeriya.

Shugaba Uhuru Kenyata,da wasu shuwagabanin Africa da wakilai daga Turai sun iso Abuja,inda jami’an tsaro masammam ma ‘yan sandan nan dubu shida suka ja daga don samu nasaran taron.

Altine Daniel, kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, tace”saboda baka ba zai zo garin ku ba a tashi a wayi gari ko wani abu ya same shi ba kaga ba zai zamo da dadi ba,so shi Sufeton ‘yan sanda Muhammad Dahiru Abubakar ya bada doka an kawo ‘yan sanda isassu kuma ko ina ka shiga a cikin gari zaka ga ‘yan sanda a wurare daban-daban saboda tsaro.”

Ta kara da cewa” don ace kada ka fita don kwana biyu saboda baki ban ga kamar akwai wani abu a ciki ba dalilin shine muna so muyi shi da kwai,kuma mutane suyi hakuri su sauna gida in an gama taro zasu iya fitowa,amma inda wanda dole ne sai ya fita to zai zama yana da takardar sheda .”

Shin mai hukumomin duniya ke ganin ribar da Najeriya da Afirka zasu samu ne daga taron,Dakta Shettima ,masanin tattalin arzikin yace fatan shine a samu wadanda zasu zuba jali.

In ba’a mantaba Najeriya ta fidda alkaluma na arzikinta na nuna cewa itace kan gaba fiye da Afirka Ta Kudu a nahiyar Afirka.

Ba shakka talakawa na cewa basu gani a kasa ba kuma wasu manyan kamfanonin masammam na sadarwa ba mallakan Najeriya bane.

Taron shima ya maida hankalin ga yara ‘yan matan makarantar Chibok inda China ta yiwa Najeriya tayin taimako kuma shugaba Jonathan ya amsa.
XS
SM
MD
LG