Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yiwuwar Amurka Da Iran Su Sasanta Ta Kara Dusashewa


Yiwuwar Iran da Amurka su sake bullo da wata sabuwa kuma tartibiyar yarjajjeniya kan makamin nukiliya ta dusashe ga dukkan alamu, a kalla a halin yanzu, bayan da shugabannin kasar Iran su ka fito kiri-kiri su ka yi shakulatin bangaro da yarjajjeniyar da aka cimma a 2015, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga ciki tun a 2018.

Zaman dardar dai na dada tsanani saboda akwai yiwuwar a kara kakaba ma kasar Iran takunkumin kasa da kasa baya ga wadanda tuni Amurka ta kakaba ma ta.

Shugaban Iran dai ya ce akwai yiwuwar tattaunawa da Amurka, to amma Shugaba Trump ba amintacce ba ne wajen batun tattaunawa da cin ma jituwa:

Shugaba Rouhani ya ce, “Da ace akwai amintattun mutane da ke jagorantar Amurka, da abin ya zo da sauki. Yayin da aka ce daya bangaren ba amintacce ba ne, abubuwa kan zama da wuya.”

Zuwa yanzu dai kasashen biyu sun kauce ma yaki kai tsaye tun bayan da Amurka ta kashe wani babban janar din sojin Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG