Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Kiranyen Sanata Melaye Daga Majalisar Dattawan Najeriya Ya Faskara


Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya tsallake rijiya da baya saboda yunkurin janye shi daga majalisar dattawa ya faskara saboda hukumar zabe da ta aiwatar da tantance masu yunkurin bata samu akalla kashi hamsin daga ciki dai ba.

Yunkurin yin kiranye ga dan majalisar dattawan Najeriya daga jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya ci tura a sakamakon rasa samun adadin kuri’un da zasu sa a gudanar da zaben yin kiranyen.

A ranar Asabar da ta gabata ne hukumar zaben Najeriya ta gudanar da aikin tantance sunayen masu bukatar ganin shi sanata din ya koma gida.

A tantancewar da ta yi hukumar zaben ta sanar cewa adadin da ta samu bai kai kashi goma cikin hamsin ba, saboda haka hukumar ta yi watsi da bukatar kamar yadda kakakin hukumar dake kula da jihar Kogi Ahmed Bagudu Biyombo ya sanar. Dokar zabe ta tanadi a samu kashi hamsin daga cikin dari kafin a iya zuwa mataki na gaba.

Kakakin ya ce yanzu komi lafiya lau bayan sun tantance sunayen masu bukatar kiranyen saboda babu wata bukatar ci gaba da yunkurin.

Mai sharhi akan al’amuran jihar Kogin Mallam Bashir Muhammad ya ce lamarin bai yi wani tasiri ba sai dai asarar kudi. Gwamnonin jiha da na tarayya duk sun yi asarar kudi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG