Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Sake Damke Sanata Dino Melaye


Sanata Dino Melaye

Ta leko ta koma ga Sanata Dino Melaye. Sa'o'i bayan sake shi da aka yi, sai kuma jami'an tsaron da su ka sake kama shi. Tun bayan da jami'an tsaron su ka killace gidansa ake ganin karshenta dai sai sun sake kama shi.

A safiyar yau Talata ne Ma’aikatan SARS suka danke dan majalisar dattijan Najeriya Sanata Dino Melaye mai wakiltar yammacin Jihar Kogi.

A cewar majiya mai karfi, an ajiye shi a wani gurin da ake ajiye masu laifi daura da tsohon ofishin babban bankin Najeriya dake kan babban titin Area1.

Wurin tsare masu laifin na SARS shine wanda aka sani da ajiyar masu manyal laifuka kamar kisan kai, sata da tsafi.

Lokacin da jaridar DAILY POST ta tuntubi dan majilsar ta waya, sun ji shi cikin damuwa, har suna jin abin da ke wakana a wajen kamar suna da hatsaniya da jami'an. Daga bisani kuma da aka sake kira, sai aka sami wayar a kashe.

A baya dai ‘yan sanda sunyi kokarin kama Senata Dino Melaye din bayan da jami’an shige da fice suka fitar dashi daga cikin jirgi akan hanyar shi ta zuwa Morocco a safiyar jiya Litinin.

Bayan da aka sake shi, bayan ka kwashe sa'o'i uku a ofgishin shige da fice dake filin jirgin saman, 'yan sanda masu dauke da makamai suka zagaye gidan dan majalisar har zuwa safiyar yau.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG