Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Tsige Gwamnan Adamawa Ya Samu Koma Baya


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Babban kotun jihar Adamawa yayi fatali da bukatar 'yan majalisar jihar da cewa a basu daman mikawa gwamnan takardar tuhuma koda ma ta kafofin yada labarai.

Yayin da kotun jihar ya zauna mukaddashin babban alkalin jihar Justice Ambrose Namadi yayi fatali da bukatar 'yan majalisar inda yace hakan ya sabawa doka.

Alkalin jihar Adamawa yayi misali da hukuncin kotun koli ne wajen yin watsi da bukatar majalisar. Duk da matsayin kotun wasu 'yan majalisar sun yi wani zaman gaggawa inda suka umarci magatakardar majalisar da ya mika takardar tuhuma ga gwamnan da mataimakinsa ta kafofin yadda labarai.

Dambarwar ta jawo cecekuce inda masana shari'a da harkokin aikin majalisa na ganin akwai abun dubawa.Wani lauya mai zaman kansa yace akwai ayar tambaya akan matakin da 'yan majalisa suka dauka. Yace idan 'yan majalisar zasu rubuta wasikar tuhuma gwamna zasu rubutawa ba kakakin majalisar ba. Akwai wani abun daban da suke so ba wai suna yi ba ne domin talakawa.Idan gaskiya a keyi ba yau yakamata a yi fadan ba domin shekara biyu ke nan da ba'a biya ma'aikata ba.

Ibrahim Baffa Waziri wani tsohon dan majalisar yace sun riga malam masallaci da yunkurinsu. Yace ba zasu ba gwamna wasikar tuhuma ba sai majalisa ta zauna ta amince da kudurin kafina a mika takarda.

To amma an ce biyo bayan sa bakin wasu dattawan jihar da sarakuna wasu 'yan majalisar dake kan gaban tsige gwamnan sun soma yin dari-dari.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG