Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Sanya Tambayar Zama Dan Kasa Lokacin Kidaya Mai Zuwa A Amurka


Sakataren harkokin cinikayya na Amurka, Wilbur Ross

Hukumar kidaya ta Amurka na tattara kiyasin adadin jama’a duk bayan shekaru 10, a shekarar 2020 za a sake yin wata kidayar.

Sakataren harkokin cinikayya na Amurka, Wilbur Ross ya sanar da cewa duk lokacin da za a sake yin kidayar jama’a a kasar za a sanya tambayar ko mutum dan kasa ne ko a’a.

A wani bayanin hukuma da ya fidda a daren jiya litinin, Ross ya ce, ya zabi ya kara da tambaya akan zama dan kasar ne bayan da ma’aikatar shari’a ta bukaci hakan, wanda ta ce matakin na da muhimmanci don samun bayanan da za su taimaka wajen aiwatar da dokokin da zasu kare hakkokin kada kuri’a na tsirarun jama’a a kasar.

Sai dai wannan matakin ya janyo suka daga wadanda suke gani tambaya akan zama dan kasa zata sa mutane ba za su shiga kidayar ba, saboda fargaban rashin sanin yadda gwamnati zata yi amfani da bayanan, abinda zai sa ba za a kirga wasu al’ummar kasar ba.

Ana amfani da alkaluman kidayar wajen tantance yawan guraben kujerun da za a ba kowacce jiha a majalisar wakilan Amurka da kuma yadda gwamnatin tarayya zata rarraba biliyoyin daloli wajen yin wasu ayyuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG