Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Binne Uwargidan Tsohon Shugaban Amurka Nancy Reagan Kusa Da Mijinta


Cibiyar adana littafai ta Reagan ta sanar da cewa, Uwargidan tsohon shugaban Amurka Nancy Reagan, shugaban kasar na arba’in Ronald Reagan, ta rasu jiya Lahadi sakamakon bugun zuciya, tana da shekaru casa’in da hudu a duniya.

Za a binne ta kusa da maigidanta a harabar dakin karatu na Ronald Reagan dake Kwarin Simi, jihar California.

Ana ta aiko da sakonni ta’aziya masu sosa zuciya saboda da rasuwar uwargidan shugaban kasar, wadda tayi suna wajen nuna matukar kauna da kusantar maigidanta da take kira Ronnie.

Micheal Reagan, shugaban cibiyar kare muraddun Reagan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “Nancy tana wurin da take so ta kasance a kullum, tare da Ronnienta, yanzu tana da salama.

Shugaba Barack Obama da uwargidansa Michelle sun fada a wata sanarawa ta hadin guiwa cewa, Nancy Reagan ta sauya matsayin uwargidan shugaban kasa, a zamaninta. Nancy Reagan ta taba rubuta cewa, babu wani abinda zaka yi da zai koyawa maka zama a fadar White House. Babu shakka abinda ta fada gaskiya ne, sai dai mun koyi darasi, domin mun yi sa’a mun ci moriyar gurbin da ta bari, da kuma shawarwarinta. Inji sakon ta’aziyar tasu.

Uwargidan tsohon shugaban kasa Barbara Bush ta fada a sakon ta’aziyarta cewa, Nancy Reagan ta yiwa maigidanta shugaba Reagan biyayya matuka, muna da kwanciyar hankali cewa, zasu sake saduwa.

Asali an radawa marigayiyar suna Anne Frances Robbins, kafin mahaifiyarta ta bata suna Nancy. Ta gaji wasan kwaikwayo daga mahaifiyarta, Marigayiyar ta yi wasan kwaikwayo a New York da kuma Hollywood, inda ta sadu da dan wasan kwaikwayo Ronald Reagan.

Sun yi aure a shekarar alib da dari tara da hamsin da biyu.

Tayi wasannin kwaikwayo a fina finai goma sha daya, na karshe shine wanda ake kira Hellcats of the Navy , wanda ita da mijinta suke ciki.

Uwargidan tsohon shugaban kasar Nancy Reagan, ta jagoranci gangamin yaki da shan miyagun kwayoyi da taken “Just Say No to Drugs” wani gangami da aka dauka da muhimmanci a matsayin kasa.

Uwargidan tsohon shugaban kasar Nancy Reagan wanda take tare da maigidanta a kowanne lokaci, an rika sukarta sabili da kazamin kashe kudi lokacin da suke fadar White House a lokacinda ake fama da rashin aikin yi.

Maigidanta tsohon shugaban kasar ya rasu a shekara ta dubu biyu da hudu sakamakon cutar mantuwa.

Suna da ‘yaya biyu, Patti Davis da Ron Reagan.

XS
SM
MD
LG