Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Daina Baiwa Daliban Firamare Abinci a Takarda


Shirin Ciyar Da Kananan Yara da Abinci a makarantun Kano
Shirin Ciyar Da Kananan Yara da Abinci a makarantun Kano

Gwamnatin tarayya za ta dauki matakan gyara a shirinta na ciyar da daliban Firamare a fadin kasar.

Yayin da makonni kadan suka rage daliban makarantun sakandare da Firamare a Najeriya su koma makaranta bayan kammala hutun shekara, mai baiwa shugaban ‘kasa shawara kan harkokin yaki da fatara tsakanin ‘yan kasar, ta ce zasu dauki matakan gyara dangane da batun zubawa dalibai abinci akan takarda karkashin tsarin ciyarwa na gwamnatin tarayya wadda ofishinta ke aiwatarwa.

A watanni da suka gabata ne, yayin da wakilin Muryar Amurka ya ziyarci wasu makarantu dake cin gajiyar shirin a Kano, ya ga yadda daliban dake cin abinci akan takarda.

Sai dai a zantawa da wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari, Hajiya Maryam Uwais ta danganta laifin akan gwamnatin jihar Kano. Tana mai cewa gwamnatin jiha ce ya kamata ta samarwa da daliban kwanikan da za a rinka zuba musu abinci, domin kudin da gwamnatin tarayya take bayarwa na abinci ne.

Kamar yadda aka shirya wannan tsari na ciyar da dalibai, shine gwamnatin tarayya zata biya masu dafa abinci kudadensu a hannunsu ba tare da an baiwa wani ya basu ba. maganar kwanikan da za a rika zuba musu abinci ya rage ga gwamnatin jiha, idan itama ba za ta iya bayarwa ba, to ta nemi daliban su rinka zuwa da kwanan abincinsu daga gida.

Domin karin bayani saurari hirar Mahmud Kwari da Hajiya Maryam Uwais.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG