Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Dawo Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna


Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna
Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta dawo da sufurin jirgin kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a watan Nuwambar 2022.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a yayin da yake jawabi kan ayyuka ma’akatar.

Wannan na zuwa ne wata guda bayan Gwamnatin Tarayya ta ce an sako ragowar fasinjojin da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jirgin kasan a ranar 5 ga Oktoba, 2022.

Ministan ya bayyana cewa an tanadi matakan tsaron ba dare ba rana ga sufurin jirgin kasan, wanda wata bakwai ke nan da dakatar da shi.

Ministan ya ce hukumarsa ta koyi darussa daga harin da aka kai wa jirgin kasa a watan Maris, lamarin da ya sa aka dakatar da sufurin jiragen kasa tsakanin manyan biranen biyu.

Ya ce an shirya jami'an tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji, to sai dai bai bayyana ainihin ranar da za a fara jigilar ba.

Haka kuma ministan ya ce an yi wani tsari da zai rika lura da zirga-zirgar jiragen kasan da kuma titin jirgin.

Ya kara da cewa, tsarin zai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ma'aikatu da hukumomin gwamnati da jami'an tsaro damar ganin abun da ke wakana a kan titin jirgin ba tare da bata lokaci ba.

Idan ba a manta ba, a ranar 28 ga Maris 2022 ne gwamnatin Tarayya ta dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna, bayan ’yan ta’adda sun kai masa harin bom suka kashe mutum 10 tare da sace wasu 60.

XS
SM
MD
LG