Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kafa Cibiyar Inganta Ayyukan Hakar Albarkatun Man Fetir A Jihar Bauchi


Kamfanin hakar mai na Chevron a Warri.
Kamfanin hakar mai na Chevron a Warri.

Gwamnatin jihar Bauchi ta kulla yarjejeniyar hadin guiwa da gwamnatin tarayya da kuma Majalisar Dinkin Duniya, domin samar da cibiyar horas da matasa, da zata tallafawa ayyukan hakar man fetir.

A yayinda aikin harkar albarkatun man fetur da kuma iskar gas ke ta gudana a jihohin Bauchi da kuma Gombe, gwamnatin Jihar Bauchi ta sanya hannu a fannoni biyu don kafa cibiyar horas da ma’aikata da zasu rinka samar da kayayyakin da kamfanin masu hakar albarkatun man fetur da kuma Iskar gas din zasu bukata.

Cibiyar zata kuma taimakawa kamfanin samar da makamashin wutar lantarki na Mambila, batun samar da kare muhalli.

Matasa da gwamnatin Gombe ta horas aikin tsaro
Matasa da gwamnatin Gombe ta horas aikin tsaro

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdukadir Muhammed ya bayana hakan ne a taron manema labarai inda yace yace, hadin gwiwa ce da gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi na cikin gida da kuma kasashen ketare.

Gwamnan ya bayyana cewa, manufar shirin shine, samar da doka da zata tabbatar da ci gaba da aiwatar da shirin. Yace dokokin za su kuma taimaka wajen inganta rayuwar al’umma kasancewa cibiyar a ake shirin kafawa a Alkaleri za ta horas da matasa wajen koyon sana’oin hannu da za su iya yi ba tare da dogara ga gwamnati ba.

Wasu Matasa A Jihar Pilato Sun Gyara Na’urar Shakar Numfashi
Wasu Matasa A Jihar Pilato Sun Gyara Na’urar Shakar Numfashi

Za a fara aiwatar da shirin ne da matasa masu ilimi sama da dubu goma a rukunin farko. Bisa ga cewar gwamnan, shirin zai kasance irinsa na farko a nahiyar Afrika baki daya.

Daga cikin sana’oin da za a rika koyar da matasa a cibiyar akwai walda, da harkokin gine gine, da shafe-shafe, da aikin kafinta da sauran sana’oi da suka jibinci aikin fetir.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti:

Za A Kafa Cibiyar Inganta Ayyukan Hakar Albarkatun Man Fetir A Bauchi-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00


Karin bayani akan: Jihar Bauchi, Majalisar Dinkin Duniya, Man Fetur, Nigeria, da Najeriya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG