Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Za a Takaita Zirga-Zirga a Ranar Zabe


'Yan Sandan Najeriya.

Shugaban hukumar zaben Najeriya ya bugi kirjin cewa duk wadanda ma suke ganin zabe ta hanuyar amfani da na'urar tantance masu zabe ba zai nasara to su sa ido su yi kallo.

Kwanaki uku gabanin babban zaben Najeriya da ke tafe a ranar 28 ga watan Maris, hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta nuna cewa ta shirya tsaf don gudanar da zaben ga masu nuna adawa da maganar na’urar tantance katin zabe na dindindin da aka ba ‘yan Najeriya akan cewa wai za a yi magudi.

Shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega ne ya bugi kirji da cewa a matsayinsa na tsohon malamin makaranta ya san cewa idan aka sami maki sittin bisa dari a jarrabawa to an ci nasara. Kila dai akwai wasu manufa ne da yasa wasu ke sukar lamarin da bai san dalilin hakan ba inji Farfesa Jega.

Shi kuwa Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya Sulaiman Abba na ganin cewa ba daidai bane idan mutum ya kada kuri’arsa ya kuma tsaya a wajen. Inda yace duk wanda ya jefa kuri’arsa to ya wuce abinsa don kar mutum ya fada tarkon dokar da aka tanada game da zabe.

Ya tabbatarwa al’ummar Najeriya cewa horon da aka bawa ‘yan sandan ya isa su yi abinda ya dace a wajen ba tare da musgunawa kowa ba matukar aka bi doka da oda. Shi kuwa wani lauya kuma dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar adawa M.A Abubakar wanda kuma tsohon babban kwamishinan hukumar yayi kira ga mata da su guji zuwa kada kuri’arsu da kunshi a hannunsu don na’urar ba zata iya kidaya zanen hannunsu ba.

Usman Usman daga Kano na kungiyar hadin kan Fulani ya kara jaddada yadda ake bin rugage ana saye katunan kada kuri’ar na Fulani kamar yadda ya faru a Barikin Ladi, Royam, Taraba wajen Jalingo da Rekam, Langtang, Jigawa Zamfara Kebbi wajen Arugungu da kuma Katsina inda har suka bada rahoton wani Kansila aka kama shi akai

Hukumar INEC tace zasu binciki lamarin yadda abin ya faru. Jami’an ‘yan sanda sun fidda sanarwa takaita zirga-zirga a ranar zaben. Sannan duk da an haramta bayyanar jami’an tsaro da wata babbar kotun tarayya a Legas tayi, tuni sojojin da dama sun bayyana a Abuja har sun kafa shigaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG