Accessibility links

Za a yi Zaman Sasanci da 'Yan Kungiyar Boko Haram a Cikin Makon Nan


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau. (File Photo)

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram sun yarda a sasanta, wasu kuma basu yarda ba.

A wannan makon ne ake sa ran sake zama da wakilin Kungiyar Boko Haram da wakilan gwamnati don sasanci.

Hassan Tukur, babban jami’I ne a fadar shugaban kasar Najeriya, ya tabbatar ma muryar Amurka cewa za a yi zaman sasantawar a cikin makon nan amma bai fadi rana ba, sabanin wasu rahotanni da suka ce yau litinin ne a za yi zaman.

Sai dai akwai shakku tattare da wasu mutane har ma da wasu jami’an tsaro akan sahihancin tsagaita wutar, ganin hare-haren da aka kai a ‘yan kwanakin nan a wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Duk da dai Malam Hassan ya ta tabbatar da cewa babu yaudara a sasantawar da akeyi, ya janyo hankali akan cewa dole ne a cikin kungiya irin wannan a sami rabuwar kawuna. Don wasu ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun fada masa cewa ba da yawun shugaban su ake sasancin ba.

Malam Hassan ya kara da cewa sasanci irin wannan wani abu ne mai wuya, amma ba shi da wata shakka akan za a cimma mafita daga karshe.

“Haka kuma ana sa ran za a warware matsalolin wasu ‘yan Kungiyar da ke kai hare-hare a zama na gaba” a ta bakin Hassan Tukur. Ya kuma jaddada cewa za a bayyana ma jama’a sakamakon yarjejeniyar ba tare da bata lokaci ba.

kammar yadda zaku ji anan, ga cikakkiyar hirar da Halima Djimrau tayi da Malam Hassan Tukur.

XS
SM
MD
LG