Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Yi Zanga-Zanga a New York Kan Kalaman Trump Game Da Afirka


Shugaba Amurka Donald Trump
Shugaba Amurka Donald Trump

Ana ci gaba da nuna bacin rai game da kalaman batancin da aka danganta su da Shugaban Amurka Donald Trump. Ko a yau dinnan Litinin, yayin da ake bukukuwan zagayowar ranar tunawa da dan rajin fafutuka Martin Luther King Jr a fadin Amurka.

Ana shirin gudanar da zanga-zanga a yau a birnin New York domin nuna bacin rai kan kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na batanci akan wasu kasashe.

Za a gudanar da zanga zangar ce yayin da ake hutun tunawa da fitaccen dan gwagwarmayan nan Martin Luther King Jr a duk fadin Amurka.

A kwanakin baya wasu kafafen yada labarai a Amurka suka ruwaito cewa Trump ya kwatanta nahiyar Afirka da Haiti a matsayin kasashen "kasakantattu."

A fadi hakan ne yayin da yake wata ganawa da wasu 'yan majalisar dokokin Amurkan kan batun shige da fice.

Kalaman na Trump sun janyo kakkausar suka daga sassan duniya musamman ma daga nahiyar Afirka.

Abokiyar aikinmu Grace Alheri Abdu, ta zanta da wani dan asalin Ghana mazaunin Amurka, Muhammadu Mada, wanda ya yi tsokaci kan kalaman da ake zargin Shugaba Trump da fada.

Latsa kasa domin sauraren hirar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG