Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Biya Ma'aikatan PHCN Kudaden Sallamar su Daga Aiki


PHCN
PHCN

Ma'aikatan PHCN dubu 20,304 za a biya kudaden sallamar su daga aiki bayan sayar da hannayen jarin ma'aikatar

Wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja Madina Dauda ta aiko ma na da rahoton cewa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saki kudade sama da Naira miliyan dubu dari da goma sha tara (N119, 176,731,492.88) domin biyan ma'aikatan kamfanin wutar lantarki ta kasa PHCN, da aka sallama daga aiki. Kakakin Hukumar sayar da hannayen jari ta kasa wato BPE Chigbo Anichebe shi ne ya sanya hannu a kan takardar sanarwar da aka rabawa ‘manema labarai a Abuja.

Madina Dauda ta ci gaba da cewa ofishin Akanta janar ne ya bayar da kudaden da za a biya ma'aikata dubu ishirin da dari uku da hudu a cikin ma'aikata dubu arba'in masu aiki a ma'aikatar ta PHCN. Tuni dai gwamnatin tarayya ta sayar da hannayen jarin ma'aikatar, wadda ta baya bayan nan ita ce ma'aikatar wuta ta Kaduna da aka sayarwa kamfanin Northwest Energy a kan kudi dolar Amurka miliyan dari biyu da sittin. Idris Danlami Mohamed shi ne shugaban ma'aikatar wuta ta kaduna, Madina Dauda ta tambaye shi ko an sayar da ma’aikatar tare da ma’aikatan ne?

Za a biya ma'aiktan PHCN Naira miliyan dubu 119, 176, 731, 492,88 - 2:31
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG