Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Bam Ya Tashi Bayan da Buhari Ya Sauka a Maiduguri


Janaral Buhari dan takarar APC

Yayinda Janaral Buhari ya kai yakin neman zabe a Maiduguri sai bam ya tashi a wata anguwa.

Lokacin da yake yiwa jama'a jawabi Janaral Buhari yace zai kawo karshen Boko Haram da duk abubuwan da suka jibanci tsaro idan aka zabeshi shugaban kasar Najeriya.

Janaral Buhari ya kuma yi alkawarin sake gina duk gidajen mutane da aka kona ko kuma aka lalata sakamakon rigingimun Boko Haram a dukanin kauyuka da garuruwan da aka lalata.

To saidai Janaral Buhari bai samu yin wani dogon jawabi ba sabili da rubibi da tarnakaki da jama'a suka dinga yi a wurin taron.

Wasu da suka yi kokarin halartar taron sun bayyana rashin jin dadinsu da abun da ya faru.Bayan sun yi addu'ar Allah ya taimaki Janaral Buhari sai suka yi korafin cewa an hanasu shiga filin taron. Jami'an tsaro su suka hana wasu mutane shiga harabar taron. Harta wasu 'yansanda ma an hanasu sabanin lokacin da shugaba Jonathan ya kai nashi ziyarar.

Janaral Buhari bai samu ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar ba kamar yadda aka shirya sabili da irin rubibin da mutane suka dinga yi.

Daga bisani an samu tashin wani karamin bam a anguwar Muramti gaf da shiga birnin Maidugurin inda ya raunata wasu mutane uku. Amma ba'a samu asarar rayuka ba.

'Yan kato da gora sun nuna rashin jin dadinsu da fashewar bam din musamman a ranar da Janaral Buhari ya kawo ziyara birninsu. Sun ce zuwansa wata rana ce ta farin ciki da bai kamata a ce bam ya fashe ba. Sun dora alhakin fashewar bam din akan wadanda suka kira bata gari da basa son a kawo karshen tashin tashina..

Ga rahoton Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG