Manufofin da suka shafi kiwon lafiya a Amurka, su ne batutuwan da aka fi mayar da hankali akansu a muhawarar da masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar Democrat suak yi.
Masu sassaucin ra’ayi sun kalubalanci Sanata Elizabeth Warren da Barnie Sanders, wadanda ke kan gaba a jerin masu niyyar kawar da shugaba Donald Trump a zaben 2020.
Da Warren da Sanders sun yi kiran da a kawo karshen tsarin kiwon lafiya da ke hannun kamfanonin inshora masu zaman kansu da ke bai wa ma’aikata miliyan 150 inshora ta hanyar ma’aikatansu.
Amma a muhawarar wacce aka yi a daren jiya Talata, an caccaki wadannan ra’ayoyin nasu kusan tun a farkon muhawarar da aka kwashe sa’o’i biyu ana yi a Michigan, jihar da ta kasance cibiyar kera motoci a Amurka.
“Ba sai mun zagaya muna fadawa rabin al’umar kasar nan cewa, inshorar lafiyar da suke amfani da ita ba a shimfida ta bisa ka’ida ba,” a cewar tsohon dan Majalisa daga jihar Maryland John Delaney.
Ya kuma kara da cewa, “wannan tsari ba shi da inganci, zai kawo cikas ga fannin na inshorar lafiya, hakan zai kuma sa a rufe asibitoci da yawa, wannan ba siyasa ta gari ba ce.”
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 08, 2023
Ana Bikin Ranar Mata A Duniya
-
Maris 01, 2023
Shirin Sojojin Amurka Na Yin Nasara A Yaki Da Kasar China
Facebook Forum