Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Atiku Ya Yi Jawabi Karon Farko Bayan Hukuncin Kotun Koli


Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli
Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yayi martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, tare da yin kakkausar suka dangane da tasirin hukuncin da kotun ta yanke a zaben 2023.

A wani jawabi na musamman ga manema labarai, da aka gudanar a safiyar yau a hedikwatar PDP da ke Abuja, Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan tasirin hukuncin kotun, yana mai bayyana abin da yake ganin na da hadari musamman wajen durkushewar aminta da bangaren shari’a da amanar da ke hannunsu na yiwa dimokradiyya da ‘yan kasa adalci.

Atiku ya cigaba da nuni da irin gudunmawa da ya bayar wajen tabbatar da dimkoradiyya a Najeriya tun zamanin soji, lamarin da ya kai ga neman ransa wanda sanadiyyar haka ya yi hijira da nufin ganin tabbata da dorewar dimokradiyya a Najeriya. Ya jaddada muhimmancin ayyukansa ba wai don bukatun kansa kawai ba, amma don tsananin damuwa ga makomar al'umma.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin kotun kolin, Atiku ya jaddada bukatar yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar domin kare sahihancin zabe a nan gaba. Ya kuma yi kira da a aiwatar da na’urar tantance masu kada kuri’a da tattara sakamakon zaben da ta zama cikin dokar kasa, sannan a kammala dukkan shari’o’in zabe kafin rantsar da wanda ya yi nasara, da kuma bullo da tsarin zabe na zagaye biyu don tabbatar da aniyar jama’a.

Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli
Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli

Bugu da kari, ya ba da shawarar wa'adin shugabancin kasa na tsawon shekaru shida, wanda za a rika karba-karba a tsakanin shiyyoyin siyasa shida na kasar, da nufin inganta daidaito da hadin kan kasa. Abubakar ya kuma jaddada wajabcin hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tabbatar da tantance sahihancin ‘yan takara da kuma bayyanawa jama’a duk wani sabani ko al’amura da suka taso daga tsarin tantancewar.

Da yake karin haske kan muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen tabbatar da martabar dimokaradiyya, Abubakar ya ba da shawarar yin gyare-gyare daban-daban da suka hada da tsarin gudanar da shari’a mai cikakken ‘yanci da cin gashin kansa, da kuma ingantaccen tsarin tantance ayyukan alkalai.

Wadannan matakan, a ganinsa, za su dawo da kwarin gwiwar jama'a kan harkokin zabe da kuma bangaren shari'a, tare da mayar da ikon zaben shugabanni ga masu kada kuri'a.

Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli
Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli

A lokacin da yake karkare jawabinsa, Atiku Abubakar ya yi kira ga matasan Najeriya da su ja gaba a fafutukar tabbatar da dorewar dimokuradiyya, inda ya bukace su da su bada gudunmawa da yin la’akari da shawarwarin da za a yi na sake fasalin zabe da tsarin mulki.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta ci gaba da fafutukar ganin Najeriya ta gyaru, inda ya jaddada cewa babu inda zai je, zai zauna a Najeriya don cigaba da gwagwarmaya da fafutakar tabbatar da adalci da ingantaccen tsarin dimokradiyya.

A tattaunawa ta musamman da Atiku Abubakar yayi da wakilan Muryar Amurka, yace shi a karan kansa yayi Allah wadai da wannnan hukunci da kotun koli tayi kuma har yanzu baiji mutum daya da ya yaba mata ba, kuma yanzu abinda ya rage shine illahirin ‘yan kasa su hadu domin ganin sun ceto kasar daga halin da take ciki musamman lura da irin hukuncin da kotun sauraren kararraken zabe da kotun koli suka yanke duk da irin shaidu da suka bayyana rashin cancantar shugaba Tinubu fitowa takarar zabe.

A nashi banageren, shugaban riko na jam’iyyar PDP, Iliya Umar Damagum ya bayyana cewa, “babban abinda ake tsoro idan rashin adalci yayi katutu a waje shine kasa zata shiga cikin rudani, amma mu a matsayin mu na ‘yan jam’iyyar PDP mutane ne masu bin doka domin ainihin jam’iyyar an gina ta a bisa doka ne, kuma idan aka yi la’akari da tun muna mulki da bamu ci zabe ba haka muka bada mulki domin Najeriya girmanta yafi muradan mu, don haka muka mika mulki don tabbatar da cigaba da zaman lafiyar kasa”

Damagun ya janyo hankali kan yadda bangaren hukumar zabe da bangaren shari’a ke kara lalacewa kamar yadda ya bayyana, yana mai cewa suna tsoro kada a kai lokacin da zai zama cin zabe sai ansa karfin tuwo ana ha maza ha mata kafin a sami nasara.

Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli
Taron Manema Labarai da Atiku Abukar Ya Kira Kan hukumcin Kotun Koli

A karshe Damagun ya bayyana cewa a bangaren su tun da ake yiwa kotun koli da lakabin kotun Allah ya isa, to suma kuwa daga bangaren su sunce “Allah ya isa”.

Yayinda aka kammala shari’ar kotun koli kuma dukkan jam’iyyun adawa sun hakura, yanzu makomar kasar ta ta’allaka ne da irin jagorancin da gwamnati mai ci zata yi musamman wajen shawo kan dimbin matsolilin da kasar ke ciki, da matsin rayuwa da tattalin arziki.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG