Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Gwamnatin Cancanta Zan Kafa Ba Ta Hadin Kan Kasa Ba-Tinubu


Shugaban APC Bola Tinubu
Shugaban APC Bola Tinubu

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kafa gwamnati mai cancanta ta kasa maimakon ta hadin kan kasa don magance kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata wasika da shi kansa ya sanya wa hannu jiya Alhamis a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa, “A matsayina na shugaban ku mai jiran gado, na amince da aikin da ke gabana. An yi maganar kafa gwamnatin hadin kan kasa, burina ya fi haka. Ina neman gwamnati mai cancanta ta kasa.

"A yayin hada gwamnati na, ba zan yi la'akari da abubuwan da suka wuce gona da iri ba. Ranar wasannin siyasa ta shude.

"Zan tattaro kwararrun maza da mata da matasa daga ko'ina cikin Najeriya don gina kasa mai aminci, mai wadata kuma Najeriya kawai."

Hukumar INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya doke abokan hamayyarsa, kamar su Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Tuni dai tsohon gwamnan jihar Legas ya karbi takardar shaidar cin zabe daga INEC.

Ana sa ran za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya nan da makonni kadan, wanda zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.

XS
SM
MD
LG