Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Rura Wutar Rikici


Janar Farouq Yahaya
Janar Farouq Yahaya

Rundunar sojojin Najeriya ta ja kunnen masu rura wutar rikici a sassa daban daban na kasar da su yiwa kansu kiyamullayli, domin kuwa rundunar zata dau duk wani matakin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata wajen ganin ta kare yan kasa na gari.

A hirar shi da Muryar Amurka, Janaral Farouk Yahaya ya jaddada cewa rundunar sojin kasar zataci gaba da yin biyayya ga kundin tsarin mulkin da Najeriya, inda ya tabbatarwa yan kasar cewa hafsoshi da sojojikn kasar baki daya za suci gaba da kare yanci da diyaucin Najeriya.

Babban Hafsan hafsoshin sojojin Najeriyar kazalika ya kuma ce zasu ci gaba da aiki tare da sauran rundunonin mayaka da sauran jami'an tsaro wajen taimakawa hukumomin fararen hula don samar da kyakkyawan yanayin gudanar da babban zaben.

Bugu da kari Shugaban sojojin ya kuma nemi sojojin da su taka rawar da ta dace wajen bin ka'idoji da tanaje tanajen da aka tsara yayin da suke aikin tallafawa samar da tsaro lokacin gudanar da babban zaben na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Masu ruwa da tsaki irinsu Bashir Dan musa na ganin wannan gargadin da rundunar mayakan ke aikewa masu rura wutar rikicin yazo daidai lokacin da ya dace musamman ganin yanzu dakarun na samun nasara kwarai da gaske akan masu tafka ta'asa a kasar.

Dan Musa yace yanzu ba lokacin yin batanci ko rura wutar rikici ba ne, don haka yunkurin sojojin ba ko shakka zai taimaka wajen samar da sauki sosai kan matsalar tsaron wanda hakan ka iya taimakawa wajen gudanar da zabubbukan na badi idan Allah ya kaimu cikin kwanciyar hankali.

Yanzu dai abin jira a gani shine irin rawar da sojin zasu taka wajen samar da kwanciyar hankali a zabubbukan na shekara mai kamawa musamman ganin sassa daban daban na kasar na fama da tarin kalubalen tsaro.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG