Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC: Yadda Zabukan Fitar Da Gwani Suka Nuna Har Yanzu Akwai Rikicin Cikin Gida A Wasu Jihohi


Abdullahi Adamu, Shugaban Jam’iyyar APC a Najeriya

A Najeriya alamu na nuna irin rashin tabbas da ake samu tsakanin ‘yan siyasa duk da kokarin da ake yi na sasanta bangarori da ke rikicin cikin gida a jam'iyyun.

SOKOTO, NIGERIA - Abin da ke nuna hakan shi ne, irin yadda ‘yan siyasar da suka shahara tare da yin suna a fagen siyasa ke fuskantar koma baya a lokutan zabuka, kamar yadda yake faruwa yanzu a jam'iya mai mulkin kasar ta APC.

Jam'iya mai mulki a Najeriya ta sha fama da rikice-rikicen cikin gida a can baya abin da har ya kai ga uwar jam'iyar ta kafa kwamitin sasantawa wanda ya yi ta shawagin jihohin da aka samu rikice-rikicen don ganin an sasanta ‘ya'yan jam'iyar.

Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar na daga cikin Jihohin da rikicin cikin gida ya yi kamari kuma ya gagara a sasanta tsakanin bangaren gwamna mai mulki yanzu Sanata Abubakar Atiku Bagudu da kuma tsohon gwamna Sanata Muhammad Adamu Aliero.

Yunkurin sasanta bangarorin dai a iya cewa ya tashi a tutar babu musamman duba da yadda zaben fitar gwani na ‘yan takarar kujerar gwamna ya gudana a jihar, inda dan takarar gefen Aleiro wanda kuma shi ne jagoran majalisa a majalisar dattawan Najeriya Sanata Abdullahi Yahaya ya kasa samun ko da kuri'a daya, yayin da shi kuwa na bangaren gwamnati ya samu kuri'a fiye da dubu daya.

Kawo zuwa hada wannan rahoton dai bangaren da aka kayar warwas bai ce komai ba, duk da yake daya dan takarar Abubakar Malam ya aminta da zaben.

A jihar Sakkwato ma jam'iyar ta fuskanci matsaloli musamman abinda ya shafi shugabancinta a matakin jiha matsalar da yake har gaban kotu.

A nan ma zaben fitar dan takara ya gudana inda jagoran bangaren da ke jayayya Abubakar Umar Gada ya kasa samun ko kuri'a daya duk da yake bai je wurin zaben ba amma kuma bai janye daga takarar ba kamar yadda dayan masu jayayya, Abdullahi Balarabe salame ya yi na aikewa da takardar janyewar sa.

Wadannan abubuwan da suka faru basu rasa nasaba da rikice rikice da ke tsakanin jagororin jam'iyar ba.

Masana kimiyar siyasa kamar farfesa Abubakar Abdullahi na jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato na ganin wadannan matsalolin suna illoli ga tsarin dimokradiya.

Yanzu dai bayan kammala zabubukan tsayar da ‘yan takarar wadanda suka samu galaba sun ayyana shirin su na kokarin samun galaba a zabubukan gaba yayinda wadanda aka kayar ke can suna nazarin matakin da zasu dauka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

APC: Yadda Zabukan Fitar Da Gwani Suka Nuna Har Yanzu Akwai Rikicin Cikin Gida A Wasu Jihohi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dubi ra’ayoyi

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG