Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Amurka: Ana Ci Gaba Da Kirga Kuri'un Jihohi


Ana ci gaba da kirga kuri'u a jihohin da ke gabar Amurka ta Gabas da duk fadin kasar, bayan da Amurkawa suka yanke shawarar ko za su bai wa shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican wani wa'adin shekaru hudu, ko kuma su mika Fadar White House ga dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden.

Miliyoyin kuri'un da aka kada jiya Talata sun karu ne kan kuri’u sama da miliyan 100 da aka jefa yayin bude runfunan zabe da wuri, yayin da Amurkawa ke zabar shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Amurka, da jami'an jihohi da na kananan hukumomi. Ana tsammanin yawan masu jefa kuri'a zai yi sama duk da rikice-rikicen da annobar coronavirus ta haifar.

A cikin sa’o’i masu zuwa, za a mai da hankali sosai ga kidayar kuri’un a jihohin Florida da North Carolina - wadanda dukkaninsu suka taimaka wajen ingiza Trump zuwa nasara a shekarar 2016, kuma inda zaben jin ra’ayin masu jefa kuri’a a wannan shekara ya nuna Trump da Biden suna kankankan da juna. Yankin gabashin jihar Pennsylvania da ake kira fagen daga, kuma shine akafi mai da hankali, amma ba lalle bane a fitar da cikakken sakamako ba har sai ya dauki tsawon kwanaki.

Masu sharhi sun ce dukkan jihohin ukun na da matukar muhimmanci ga Trump idan har yana son wa’adi na biyu, kuma ya guji zama shugaban Amurka na uku a cikin shekaru arba’in da suka gabata da ya fadi neman sake tsayawa takara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG