Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar da Mata Ke Takawa a Zaben Amurka


Wata mata lokacin da ta kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Amurka na 2020
Wata mata lokacin da ta kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Amurka na 2020

Mata a Amurka suna taka muhimmiyar rawa a zaben shugaban kasa, sukan kuma gudanar da gangami a duk fadin kasar gabanin zabe da nufin fadakar da ‘yan’uwansu kan muhimmancin zaben

Shekaru 100 bayan dokar da da ta ba mata ‘yancin yin zabe, mata masu kada kuri’a na tasiri sossai a zabukan Amurka.

A duk zabukan shugaban kasa na Amurka da aka yi tun daga shekarar 1964, an samu karin mata fiye da maza da suka kada kuri’a kuma tun daga shekarar 1980, jinsunan biyu sun sha bamban sosai a ra’yoyinsu na kada kuri’a.

Gangamin mata a Washington, DC, 01.21.2017
Gangamin mata a Washington, DC, 01.21.2017

Helen Bako, ‘yar Najeriya ce da ke zama a jihar California a Amurka, ta ce mata na taka muhimmiyar rawa sosai a zabukan kasar tun bayan da suka samu yancin kada kuri’a.

Ta ce…. “mata bakar fata musamman masu ruwa da tsaki a jami’iyyar Democrat sune ke karfafa gwiwar mata ‘yan uwansu da ma sauran jama’a akan su fita yin zabe.”

Helen Bako
Helen Bako

Wani binciken jaridar Bloomberg ya nuna cewa mata sun fi maza zaben ‘yan takara daga jam’iyyar Democrat, musamman ma an fi ganin bambancin ra’ayin a lokacin gwamnatin shugaba Donald Trump.

A nasarar ban mamakin da ya samu a zaben shekarar 2016 lokacin da ya kara da Hillary Clinton, mace ta farko da ta tsaya takarar Shugban kasa a jam’iyyar Democrat, Trump ya samu kuri’un maza kashi 52 cikin 100 mata kuma kashi 41. Wannan gibin na kashi 11 shine mafi yawa da aka taba samu a tarihin zaben shugaban kasa cikin karni 4 da suka gabata.

Dangane kuma da abinda ya sa mata da maza su ke da bambancin ra’ayi, a zaben yan takara, da kuma abinda hakan ya ke nufi sai Helen Bako ta bayyhana cewa,….. “Yawanci lokuta jam’iyyar Democrat ta fi ba mata zarafi su tsaya takara ba kamar jam’iyyar Republican ba. Ta kuma ce a zaben na bana mata da yawa sun fita kada kuri’a, musamman mata matasa.”

mata-sun-gudanar-da-gangamin-kira-a-fita-zabe-a-fadin-amurka

shugaba-trump-zai-zabi-mace-a-matsayin-alkali-a-kotun-koli

biden-ya-zabi-mace-bakar-fata-a-matsayin-mataimakiyarsa

Bambancin ra’ayi tsakanin jinsin maza da mata da aka samu wajen kada kuri’a karon farko shine a zaben shekarar 1980, lokacin da Ronald Reagan, ya karfafa batun hana zubar da ciki, batun da har yau ake takaddama akansa.

Wani bincike na baya baya da aka yi ya gano cewa gibin da ake samu a jinsin mata da maza wajen kada kuri’a na da nasaba da karfin tattalin arzikinsu da kuma yadda siyasara Amurka ta raba manyan jam’iyyun kasar biyu akan wasu muhimman batutuwa, kamar na yan ludu da madigo, taimakawa masu karamin karfi, da kiwon lafiya.

Elizabeth Kingsbury lauya ce da ke zama a birnin Washington, Ta ce jam’iyyar Republican ta zaba a shekarar 2012 saboda yin la’akari da yadda ‘yan Republican ke daukar batutuwan mata.

Ta ce…… “a ganina a duk lokutan zabe jam'iyyar Repblican na so ne ta tauye hakkokin mata da muka yi gwagwarmayar samu shekaru da dama da suka wuce.”

Duk da mabambantan ra’ayoyin da ake samu tsakanin jinsin maza da na mata ba dukkan mata bane ke ra’ayin jam’iyyar Democrat.

Gangamin mata a Washington, DC
Gangamin mata a Washington, DC

A watan Mayun shekarar 2019, wasu mata sun yi gangamin nuna goyon bayan Shugaba Donald Trump a birnin St. Louis park da ke jihar Minnesota a karkashin jagorancin Mary Susan Timion.

Ta ce….. “mun tattaru nan ne don mu nuna jin dadinmu akan shugaba Donald Trump, mata na son Trump shi ya sa muke so kowa ya ga ni. Ta kara da cewa ita da sauran mata da yawa sun yarda da manufofin Trump.”

A shekarar 2018, wani binciken jin ra’ayoyin jama’a ya gano cewa kashi 45 cikin 100 na mutane a Amurka na fatan za a zabi mace a matsayin shugabar kasa a zamaninsu. Kusan kashi 51 na mata, sun ce suna fatan hakan zai faru idan aka kwatanta da maza kashi 38.

Saurari rahoton cikin sauti:

Rawar da mata ke takawa a zaben Amurka-4:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG