Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Rasha: Ba a Bai wa Masu Kada Kuri'a Zabi Mai Yawa Ba - OSCE


Wasu 'yan kasar Rasha a lokacin da suke kada kuri'a
Wasu 'yan kasar Rasha a lokacin da suke kada kuri'a

An kammala zaben shugaban kasa a Rasha, kuma rahotanni na nuna alamun shugaba Vladimir Putin ne zai lashe zaben. Sai dai kungiyar tsaro da hadin kasashen turai ta OSCE, ta ce ba a bai wa masu kada kuri'a cikakken damar yin zabi ba.

Hukumar Tsaro da Hadin Kan Kasashen Turai, OSCE, ta tabattar da cewa an gudanar da zaben shugaban kasar Rasha a cikin tsanaki da adalci.

Sai dai ta ce ta lura ba’a bai wa mutanen kasar zabi mai yawa ba, na mutanen da za su iya zaba.

Wakilan da Hukumar ta tura don su yi nazarin zaben sun dawo mata da rahoton da ke cewa, yayin da aka yi ta karfafawa mutane su fito su jefa kuri’a, kuma suka fito din, sai dai takaitawar da aka yi na ‘yancin al’umma da kuma kayyade yawan ‘yan takara, sun takura wa zaben, da yake ba masu jayayya da yawa a cikinsa.”

Yanzu haka dai duk alamu na nuna cewa shugaban Rasha din na yanzu, Vladimir Putin, ya kama hanyar samun nasara a kan wasu abokan takararsa su bakwai da suka tsaya zaben shugaban kasar.

Shugaba Putin ya yi wa dubban magoya bayansa jawabi a birnin Moscow, inda ya gode musu kan jefa masa kuri’a.

Da aka tambaye shi ko zai sake neman karin wa’adin shugabanci a zaben shekarar 2030, Putin, dan shekaru 65 da haihuwa, ya ce, “wannan maganar banza ce, kuna zaton zan zauna a nan har sai na shekara 100?”

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG