Accessibility links

A ranar asabar mai zuwa Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa inda a karon farko jam'iyya mai mulki ta PDP za ta fuskanci babban kalubale da ba ta taba gani ba tun da aka koma tsarin dimokradiya a shekarar 1999.

Yayin da Najeriya ke fuskantar zabuka a ranar Asabar mai zuwa, Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama a baya ta fuskar siyasa.

Yanzu haka jam’iyya mai mulki ta PDP na fuskantar babban kalubalen da ba ta taba ganin irinsa ba a baya tun da kasar ta koma mulkin dimokradiya a shekarar 1999 inda za ta nemi kuri’un jama’a tsakanin ta da babbar jam’iyyar adawa ta APC.

Akalla jam’iyyu uku ne suka hada kai domin kafa jam’iyyar ta APC, a shekarar 2013, wanda hakan shi ne karon farko da aka samu haka a kasar, da farko wasu ma na ganin cewa sabuwar jam’iyyar ba za ta yi tasiri ba.

Amma duk da haka sai ga shi wasu mambobin jam’iyyar ta PDP na canja sheka zuwa jam’iyyar ta APC. A lokaci guda gwamnoni biyar suka tsallaka zuwa jam’iyyar, sai kuma ‘yan majalisar wakila 37, kana wasu ‘yan majalisar dattawa 11 su ma suka canja sheka.

Sai dai PDP ta dakile wannan kwarara da mambobinta ke yi zuwa APC bayan da ta nada sabon shugaba a wani mataka na sasanta ko kuma farantawa wadanda ke da korafi.

Daga baya ne kuma sai canja shekar ta yi harshen damo inda aka samu wasu ‘yan APC ma suna komawa PDP.

Har izuwa yanzu da ya rage kwanaki kadan a tafi rumfunan zabe wasu na ci gaba da canja sheka inda duk bangarorin ke ganin samu da rashi.

Masu fashin bakin siyasa sun ce, sakamakon zaben shugaban kasa zai kara azazzala canja shekar kafin a gudanar da na gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da za a yi a ranar 11 ga watan Aprilu.

“Za ka ga munate babu kunya babu tsoro suna canja sheka zuwa jam’iyyar shugaban kasar da aka zaba.” In ji Dawn Dimowo, wata mai fashin bakin a fannin siyasa.

A ganin ta nasarar da jam’iyyar adawa ta samu na karin mambobi na da nasaba da irin lokacin ta yi amfani da shi.

“Sun yi amfani da rikicin da PDP ta ke ciki domin a lokacin akwai wadanda su ke a shirye su fice daga PDP su koma APC, hakan ya basu wata dama mai kyau.” In ji Dimowo.

Daya daga manyan batutuwan da ya fara haddasa fitina shi ne cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya sabawa yarjejeniyar da jam’iyyar ta PDP ta kulla na cewa za a yi mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu.

Wasu na ganin arewa na bin bashin wa’adi a lokacin da Jonathan wanda ya fito daga kudancin kasar ya yi takara.

Sai dai wani malamin kimiyyar siyasa a Najeriyar Kabiru Mato, ya ce jam’iyyar ta APC na tafiya ne da guguwar canji.

“A hankali mutane suna kaucewa siyasar kabilanci da addini da bangaranci zuwa neman dimokradiya da za ta samar da canji. Saboda haka, ni ina ganin hakan wani abu ne da ke nuna cewa mutane suna da zabi idan sun ga wani abu bai yi musu ba.” In ji Mato.

Sai dai a daya bangaren shugaba Jonathan ya nuna halin ko-in-kula da canja shekara da wasu ke yi daga PDP zuwa APC inda ya ce haka siyasa ta ke.

“A siyasa babu aboki na dindindin, babu kuma makiyi na dindindin amma kuma akwai ra’ayi na dindindin.” In ji Jonathan.

APC dai na da rinjaye a majalisar kasar sannan tana da 14 daga cikin gwamnoni 36 na kasar, sai dai kuma Jonathan na da damar nan ta kasancewarsa a matsayi na shugaba mai ci.

Baya ga haka wasu na ikrarin cewa karin makwanni shida da aka yi, ya baiwa PDP wata garabasa, yayin da wasu ke ganin tantance wanda zai lashe zaben tsakanin manyan ‘yan takarar biyu zai yi wahala.

Kamar yadda bayani suka nuna a shekarar 2011 dan takarar APC Muhammadu Buhari ya samu dimbin kuri’u a arewacin kasar sai dai ba haka ne ya kasance a kudancin kasar ba.

Sai dai wasu na ganin APC ta yi tukin tsaye a wannan karo, inda mai fashin baki Dimowo ta ce hankalin ta ya na kudancin kasar.

“Buhari zai samu kuri’u da dama a kudancin kasar a wannan karo fiye da shekarar 2011, hakan kuma tamkar hambarar da PDP ne daga tushen ta, saboda haka wannan abin a tsaya a ga yadda zai kaya ne.” In ji Dimowo.

Jam’iyyar ta APC dai ta dauki wannan zabe ne a matsayin matakin yin waiwaye kan shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulkin Najeriya.

Kuma alamar jam’iyyar ita ce tsintsiya wadda ke nuna cewa ana bukatar a share wani abu, sai dai wasu da dama na tunanin cewa shin ko akwai banbanci tsakanin APC da PDP, ganin cewa APC na dauke da wasu ‘yan PDP, kuma akwai yuwuwar wasu ma za su shiga jam’iyyar idan Buhari ya kafa gwamnati.

XS
SM
MD
LG