Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zai Zama Abin Takaici Idan Rasha Ta Ki Amincewa Da Shirin Tsagaita Wuta - Rubio


Russia Ukraine War Saudi Arabia
Russia Ukraine War Saudi Arabia

Kremlin ta ce tana jiran karin bayani daga Washington kan wannan shirin tsagaita wuta na kwanaki 30.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya fada a ranar Laraba cewa zai zama “abin takaici matuka” idan Rasha ta ki amincewa da tayin tsagaita wuta na kwanaki 30 da Washington ke mara wa baya a yakinta da Ukraine.

Rubio yana magana ne da ‘yan jarida a Ireland, kwana guda bayan jami’an Amurka da Ukraine sun cimma yarjejeniya a Saudiyya kan tsagaita wuta na kwanaki 30 da Rasha.

Rubio, wanda ya halarci tattaunawar a Jeddah, ya ce yanzu Amurka za ta mika wannan tayin ga Rasha, kuma duk abin da zai biyo baya yana hannun Moscow.

“Za mu ga amsar da za su bayar, idan sun ce eh, to mun san cewa mun samu ci gaba mai ma’ana, kuma akwai damar samun zaman lafiya. Idan sun ce a’a, hakan zai zama abin takaici matuka kuma zai bayyana ainihin manufofinsu.”

Bayan tattaunawar a Saudiyya, Amurka ta janye dakatarwar da ta yi kan bayar da taimakon soji da mba da bayanan sirri ga Ukraine, kuma Kyiv ta nuna cewa kofa a bude take don tattauna batun tsagaita wuta da Rasha.

A yayin da Kremlin ta ce tana jiran karin bayani daga Washington kan wannan shirin tsagaita wuta na kwanaki 30, gwamnatin Trump ta dauki matakin janye dakatarwar taimakon soji da bayanan sirri ga Ukraine—a sauyi mai girma daga mako guda da ya gabata, lokacin da ta dakatar da taimakon domin matsa wa Shugaba Volodymyr Zelenskyy lamba ya shiga tattaunawar kawo karshen yakin da dakarun Rasha ke yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG