Accessibility links

Zamu Shawo Kan Matsalar Ta'addanci da Fashi da Satar Mutane - inji Jonathan


Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya jaddada burin gwamnatin kasar na gani ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ya gallabi sassan kasar, da suka hada da na ‘yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, da na satar mutane, da kuma fashi da makami.

Goodluck Jonathan yayi wannan ikirari ne jiya Asabar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauci, a taron gangamin da jam’iyyarsa ta PDP ta shiryawa shiyyar arewa maso gabas, da aka yi wa lakabi da sunan “Gangamin hadin kai na PDP” domin dinke barakar dake jam’iyyar.

Sai dai mutane kamar Garba Tela Gana na fassara ziyarar da shugaban ya kai jihar Bauci, tamkar wani aiki ne mara tasiri.

Garba Tela yace “tunda mutumin nan ya san ba sonsa ake ba, ai kamar tallan gunkin Annabi Ibrahim ne”.

Mr. Tela ya dora wa wasu mutanen arewacin kasar alhakin zabar shugaban da yake adawa da shi. Yace “mutanen arewa kam, ba akwai rubabbu ba wadanda su suka fara jefamu a cikin wannan halaka da halin ha-ula’I da muke ciki”.

Amma Dantani G.O Zuru, shugaban kungiyar gammayar samarin arewa da kuma ta kudu masu son ganin Jonathan ya zarce, ziyarar ta zumunta ce a wajensu.

Dantani yace “abinda nake so, ai a matsayinshi na shugaban kasa, ya zone domin ai a jam’iyyance, yana da kyau idan kana da jama’a ka dinga waywayensu.

Tawagar Shugaba Goodluck Jonathan ta hada da mataimakinsa Namadi Sambo, da shugaban jam’iyyar PDP Ahmed Adamu Mu’azu, da ministoci da kuma ‘yan majalisar wakilai ta tarayya.
XS
SM
MD
LG