Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Biya Duka Bashin Da Ake Bin Aminu S. Bono – Aisha Humaira


Aisha Humaira (Instagram/Aisha Humaira/BelloKano)
Aisha Humaira (Instagram/Aisha Humaira/BelloKano)

“Idan so samu ne ma, kafin a yi jana’izarsa in sauke masa duk wani nauyi da ke kansa matukar bai fi karfina ba.” Humaira ta ce.

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da ke arewacin Najeriya, Aisha Humaira, ta yi alkawarin biya wa marigayi Aminu S. Bono dukkan bashin da ake bin sa.

A ranar Litinin Bono, wanda jarumi ne kuma Darekta a masansa’antar ta Kannywood ya rasu.

Rahotanni sun ce Bono ya dawo daga aiki ya ce ba ya jin dadi, jim kadan bayan hakan kuma rai ya yi halinsa.

“Sakamakon haka, ina kira ga dukkan wanda ya san cewa ya yi wata mu’amullar kudi da shi ko bashi, ko kuma ya karbi wani abinsa bai biya ba, in sha Allahu Rabbi, in dai har bai fi karfina ba, na yi alkawari in sha Allahu Rabbi zan sauke masa nauyi.” In ji Aisha Humaira.

Marigayi Aminu S. Bono (Instagram/Aminu S. Bono)
Marigayi Aminu S. Bono (Instagram/Aminu S. Bono)

Bisa tsari na shari’ar Musulunci, ana so a biya wa dukkan wani mamaci bashin da ake bin sa kafin a binne shi.

“Idan so samu ne ma kafin a yi jana’izarsa in sauke masa duk wani nauyi da ke kansa matukar bai fi karfina ba.” Humaira ta kara da cewa.

Ta kara da cewa idan kuma har ya fi karfinta, za ta bi hanyar da za a sama masa taimako don a biya bashin.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo mai tsawon minti uku da dakika 53 wanda ta wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Litinin tana zubar da hawaye.

Marigayi Nura Mustapha (Waye)
Marigayi Nura Mustapha (Waye)

Humaira wacce ta yaba da kyakkyawar halayya irin ta marigayin, ta kuma roki dukkan wani da ya san cewa Bono ya saba masa da ya yafe masa.

“Kuma ina roka masa gafara daga dukkan wani wanda ya san Bono ya saba masa ko ya taba bata masa rai, yana sane ko ba ya sane.”

A ranar Talata ake sa ran za a yi jana'izar Bono a birnin Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rasuwar Bono na zuwa ne sama da shekara guda bayan mutuwar darektan fim din “Izzar So” mai dogon zango, Nura Mustapha Waye, wanda shi ma Allah ya yi wa cika wa ta irin makamancin wannan yanayi na mutuwar farar daya.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG