Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Magance Matsalar Rashin Tsaro Idan Na Sami Nasarar Zama Shugaban Najeriya - Gwamna Wike


Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribas.
Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribas.

Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribas, ya bayyana cewa zai magance matsalolin tsaro a Najeriya idan ya sami nasarar dare kan kujerar a babban zaben shekarar 2023 mai karatowa.

Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar PDP a jihar Binuwai a wata ziyara da ya kai wa takwaran aikinsa, Samuel Ortom.

Gwamna Wike, wanda ya bayyana aniyarsa a birnin Makurdi na jihar ta Binuwai bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a ranar Lahadin da ta gabata, ya jaddada cewa babban abin da zai sa a gaba, idan ya sami nasara, shi ne magance matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan da kuma tabbatar da bin doka da oda.

Wike ya mika godiyarsa ga mutanen jihar Binuwai da suka karbe shi hannu biyu, ya kuma yi magana da su ya na mai cewa rade-radin da ke yawo na cewa zai tsaya neman takarar shugabancin kasar a fili yake.

A cewar sa, a Jihar Binuwai ne ya bayyana aniyarsa a karon farko a fili saboda alaka ta musamman da su inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya tabbatar da rade-radin; shi ya sa ya fito fili ya sanar da hakan a jihar Binuwai domin yana da dangantaka ta musamman da jihar kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri ya bayyana.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida kan abin da zai yi na daban idan aka zabe shi Shugaban kasa, Gwamna Wike ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru wajen magance matsalar rashin tsaro a zahiri ba a baki kawai ba.

Haka zalika, Wike ya ce idan aka zane shi zai samar wa manyan hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro kayan aiki da abubuwan karfafa mu su gwiwa don sauke nauyin da tsarin mulki ya dora musu amma a bisa sharadin wa’adin da za su magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita domin gwamnatinsa ba za ta laminci uzuri ba.

Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai kan filin jiragen sama na Kaduna a karshen mako, ya ce ‘yan Najeriya na bukatar shugaba da zai magance matsalar rashin tsaro a kasar cikin gaggawa.

Kazalika, Wike ya bayar da tabbacin cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta samar da doka da oda domin a samu karin masu zuba jari daga kasashen waje kai tsaye zuwa cikin kasar.

A cewarsa, rashin bin doka da oda da gwamnatin Najeriya, karkashin jagorancin shugaba Buhari, na daya daga cikin dalilan da ke jawo fargaba ga masu zuba hannun jarin kasashen waje kai tsaye a kasar wanda ke tarnaki ga bunkasar tattalin arzikin kasar.

A halin da ake ciki kuwa, gwamna Wike ya zargi wasu ’yan takarar shugaban kasa da suka nuna sha’awarsu ta samun tikitin jam’iyyar ta PDP da cewa su ne suka haddasa faduwar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2015.

A yayin da yake neman goyon bayan wakilan jam’iyyar ta PDP gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar, gwamnan ya ce ya na da duk abin da ake bukata domin kayar da jam’iyyar APC daga kan karagar mulki idan aka bashi tikiti a jam’iyarsa

XS
SM
MD
LG