Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Shiga Daji Don Fafatawa Da ‘Yan bindiga  – Gwamna Bagudu


Abubakar Atiku Bagudu (Facebook/Kebbi State)
Abubakar Atiku Bagudu (Facebook/Kebbi State)

“Wanda bai sani ba ya sani, Hassan Mai Daji kanin mahaifiyata ne. Saboda haka, na kira gayya za mu shiga daji.”

Gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce lokaci ya yi da za su yi gayya su shiga daji don tunkarar ‘yan fashin daji da ke sace masu yara, yana mai cewa abin ya kai makura.

“Ku koma gida, ku gayawa kowa zan kira gayya.” Bagudu ya fada a gaban dandazon mafarauta da suka kai masa ziyara a fadarsa wadanda suka barke da tafi da kirari da suka ji kalaman nasa.

“Ba da wasa nake wannan magana ba, kai na ma kira gayya.” Bagudu Ya kara da cewa.

“Zan yi magana da shuwagabannin tsaro kuma za mu shiga daji, kuma za mu gayawa jihohin makwabta mu hadu a daji.”

“Don haka mun yarda, in Allah ya ga dama kila lokacinmu ne ya yi, amma duk mai daukanmu (garkuwa da mu) da yaranmu muna da rai ya yi karya.”

“Wanda bai sani ba ya sani, Hassan Mai Daji kanin mahaifiyata ne. Saboda haka, na kira gayya za mu shiga daji.”

Gwamna Bagudu ya yi wadannan kalaman ne a ranar Asabar a gaban takwarorin aikinsa na jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru da na Ekiti, Kayode Fayemi, wadanda suka kai masa ziyarar jajen sace daliban sakandare da aka yi a jihar a kwanan nan.

Kalaman nasa sun bayyana ne a wani hoton bidiyo mai tsawon minti 2:13 da ya karade shafukan sada zumunta.

“Dama Qur’ani aka ba mu muka yi rantsuwa, kuma da aka ba Badaru, bai yi rantsuwa don ya zauna a cikin ofis ba, da aka ba Kayode Fayemi littafin Bible, bai yi rantsuwa don ya zauna a cikin ofis ba, da aka ba Atiku ya yi rantsuwa ba rantsuwa na yi don aikin ofis ba, ba mu daukan abin zai kai ga haka ba, amma ta kai” In ji Bagudu.

A ranar Alhamis ‘yan bindiga suka far wa makarantar sakandaren tarayya da ke Yauri suka yi awon gaba da dalibai da dama.

A wani artabu da jami’an tsaro suka yi ‘yan fashin dajin a ranar Juma’a, rahotanni sun ce an yi nasarar kubutar da biyar daga cikin daliban wadanda wasu rahotannin suka ce yawansu ya kai 80.

A sanadiyyar hakan har an kashe dalibi daya.

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin arewa maso yammaci da suka jima suna fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare a duk lokacin da suka bushi iska.

Wasu daga cikin jihohin sun yi yunkurin yin sulhu da ‘yan bindigar amma abin ya ci tura.

Gwamnatin tarayya ta sha fadin cewa tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar tsaron musamman ta garkuwa da mutane.

Cikin kasa da mako biyu, an sace daliban makarantar Islamiyya sama da 100 a jihar Neja, sai kuma wasu dalibai da malamai takwas da aka sace a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli baya ga wadannan na Yauri da aka sace.

XS
SM
MD
LG