Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa A 2023 - Yariman


Ahmad Sani Yariman Bakura.
Ahmad Sani Yariman Bakura.

Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce zai fito takarar shugaban kasar Najeriya a zaben shekara ta 2023, muddin jam'iyyarsa ta APC ba ta tsara ba da takarar ga yankin kudancin kasar ba.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, ya bayyana goyon bayan sa 100 bisa 100 ga batun tattara sakamakon zabe ta na’urar yanar gizo inda ya ce akwai bukatar yin amfani da fasahar zamani don tsaftace tsarin zabe a Najeriya.

Kalaman na Sanata Yariman na zuwa ne biyo bayan rahotannin da suka mamaye kafafen yada labarai na baya-bayan nan da ke nuni da cewa an cire sashin da ya bada dama ga hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta tattara sakamakon zabe ta na’ura daga dokar zaben shekarar 2021 da aka yiwa kwaskwarima saboda aikin zartar da dokar da ke gaban majalisun dokokin kasar.

Ana zargin cewa ba bu wani tanadi na tattara sakamakon zabe ta na’ura a cikin sashe na 50 sakin sashi na 2 na dokar zaben da ke gaban majalisa a halin yanzu.

Sashe na 50 sakin sashi na 2 din dai, ya ce yin zabe a karkashin wannan kudurin zai kasance daidai da tsarin da hukumar INEC ta yanke, wanda zai iya hadawa da kada kuri'a ta na’ura matukar hukumar INEC ba za ta yada sakamakon zaben ta hanyar na’ura ba.

Karin bayani akan: INEC, jihar Zamfara, APC, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Yariman ya ce ya zama wajibi Najeriya ta bi sauyin da ake samu ta fuskar cigaba na zamani a duk fanonni.

Haka kuma, Sanata Yariman ya bayyana aniyar sa na tsayawa neman takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, yana mai cewa kundin tsarin mulkin kasar da ma na jam’iyyar APC mai mulki sun ba shi damar tsayawa neman takara, saidai ya jadada cewa, idan jam’iyyarsa ta yanke shawarar kai tikitin shugaban kasa kudu, zai mutunta matakin.

A game da matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, Sanata Yariman, ya ce a da ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa daukan mataki kan yanayin da ake ciki duba da rudanin da wasu gwamnoni suka sanya shi a ciki inda wasu suka bada shawarar yin sulhu wasu kuma suka ki amince da sulhu din.

Ya kara da cewa a yanzu shugaban ya tashi tsaye da manufar murkushe duk wanda aka kama da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba kai tsaye.

XS
SM
MD
LG