Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga Ba Ta Hana Gasar Sarauniyar Kyau Ba


'Yan shiga gasar sarauniyar Kyau

Duk da zanga-zangar da Musulmin Indonesia ke yi a kasar za a yi gasar sarauniyar kyau ta duniya

A yau asabar sarauniyoyin kyau na kasashen duniya daban-daban za su baje kyan su a Bali, kasar Indonesia, duk kuwa da makonnin da aka yi ana yin zanga-zanga da kuma kashedin da ofisoshin jakadancin suka yi ta gabatarwa cewa mai yiwuwa ne masu tsattsauran ra'ayi su kai hari a lokacin da ake bikin zaben sarauniyar kyan ta duniya.

Da farko a Jakarta babban birnin kasar Indonesia aka shirya yin gasar ko takarar ta bana, amma daga bisani saboda dalilan tsaro aka canza wuri, aka maida yin gasar tsibirin Bali na shakatawa da bude ido inda 'yan kabilar Hindu suka fi yawa.

Musulmi masu tsattsauran ra'ayi sun yi zanga-zangar bayyana kin amincewar su da shirya gasar a Indonesia, kasa mafi yawan al'ummar Musulmi a duniya.

Masu zanga-zangar sun ce tamkar cin mutunci ne da rashin kunya a kwashi matan da ke sanya 'yan kampai da 'yan tara-mama, da kuma matsattsun rigunan da ke nuna surar jikin su, a kai su kasar da al'ummar Musulmi ta fi yawa

Duk da matakin canza wurin da aka dauka, har yanzu akwai fargabar cewa Musulmi masu tattsauran ra'ayi na iya yin kokarin katse hanzarin ci gaba da yin bikin. Ofisoshin jakadancin kasashen Australia da Birtaniya da kuma Amurka sun gabatar da kashedi ga 'yan kasashen su da ke shirin zuwa Bali a lokacin gasar ko takarar zaben sarauniyar kyan ta duniya, suka ce su yi hattara domin akwai yiwuwar cin karo da gagarumar zanga-zanga ko ma hare-hare.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG