Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Almundahana: 'Yan sanda Sun Je Gidan Netanyahu Bincike


Shugaba Benjamin Netanyahu na Isira'la

Zargin almundahanar da ake ma Firaministan Isira'ila Benjamin Netanyahu ya dau wani sabon salo, bayan da 'yan sanda su ka je gidan Netanyahu don gudanar da bincike.

‘Yan sanda na tambayoyi ma Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu a karo na farko, a matsayin wani bangare na binciken da aka masa game da almundahanar da ta shafi kamfanin sadarwar kasar mai suna Bezeq, a cewar kafafen labaran Isira’ila.

Gidan rediyon rundunar soji da sauran kafafen labarai sun ce ‘yan sanda sun danna cikin gidan Netanhayu yau dinnan Jumma’a, a yayin da kuma ake ma matar Netanyahu, Sara, tambayoyi a wani wurin.

‘Yan sanda sun ce dandalin ‘intanet’ na Bezeq, mai suna Walla, na bayar da rahotani masu daukaka Netanyahu da matarsa, a madadin samun alfarma daga jami’an sa ido kan harkar sadarwa.

Wannan shi ne karon farko da Netanyahu, wanda ya rike mukamin shugaban fannin sadarwa har zuwa bara, ya sha tambayoyi kan wannan al’amari, wanda ake kira Batu Na 4000.

A makon jiya, an kama wasu na kusa da Netanyahu su biyu, saboda zargin su na kokarin samar da wata alfarma ma kamfanin na Bezeq ta miliyoyin daloli.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG