Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Afrika Sun Yi Zanga Zanga A Isra'ila


Masu Zanga Zanga
Masu Zanga Zanga

Kimanin masu zanga zanga dubu daya da dari biyar a manyan titunan birnin Tel Aviv na kasar Isra’ila, jiya Asabar ne suke bayyana adawarsu ga mayar da yan Afrika masu neman mafaka zuwa kasashensu, wanda galibinsu sun fito ne daga kasashen Sudan da Eritrea.

An gudanar da zanga zangar ne a kudancin Tel Aviv inda galibin mazauna wurin yan Afrika ne, da suka shigo birnin ta wata tashar motocin bos bos dake wurin. Sama da shekaru goma sha biyu, an kiyasta yan Afrika dubu arba’in ne suka shiga kasar Isra’ila ba bisa ka’ida ba.

A farkon wannan mako, Isra’ila ta fara tsare yan Afrika da suke neman mafaka da suka ki yarda taimakon kudi da Isra’ilan zata basu domin basu kwarin gwiwan su koma kasashensu da ya kai dala dubu uku da dari biyar da kuma kudin jirgi zuwa kasashen nasu a Afrika. Wadanda suka ki tafiyar zasu iya huskantar dauri na sai baba tagani.

Tuni aka daure irin wadannan yan gudun hijirar a cikin wannan mako.

Gwamnatin Isra’ila tana daukar wadannan mutane a matsayin bakin haure da suka zo neman kudi amma ba don ana nemansu a kashesu a kasashensu ba. Amma wasu yan kasar Isra’ila masu goyon bayan bakin haure sun shiga zanag zangar ta jiya Asabar tare da masu neman mafakar, suna rike da kwalaye masu rubutu cewa, babu batun kora kuma dukkaninmu yan adama ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG