Accessibility links

Zargin Da Akewa ‘Yan Sanda Kan Mutuwar Farfesa Mustapha Ahmad Falaki


Nigeria Elections

Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta musanta ikirarin da kungiyar malaman Jami’o’in kasar tayi cewa, ‘yan sanda ne sukayi musabbabin mutuwar Farfesa Mustafa Ahmad Falaki na Jami’ar Ahamadu Bello Zaria.

Bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kwace motarsa bayan sun kai hari ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Kibiya a jihar Kano, cikin watan farerun bana.

Haka zalika rundunar ‘yan sandan ta fada cewa, a cikin wani sakamakon kwarya-kwaryan bincike data gudanar ta kama biyu daga cikin ‘yan kungiyar ta Boko Haram da kuma wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hallaka Farfesa Ahamd Mustafa Falaki.

AIG Tambari Mohammed Yabo shine mataimakin Sifeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya dake Kano, shine ya yiwa Wakilinmu Muhammud Ibrahim Kwari daga Kano karin bayani. Saurari bayanin.

XS
SM
MD
LG