Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Ayyana Dokar Hana Yawon Dare A karamar Hukumar Karu A Jihar Nassarawa- Oktoba 24, 2022


Nasiru Adamu El Hikaya
Nasiru Adamu El Hikaya

Shirin na wannan makon tattaunawa da matasa ne na karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa biyo bayan ayyana dokar hana yawon dare don dakile kutsowar ‘yan ta’adda da sauran miyagun iri a yankin wanda bayanan sirri na jami’an tsaro su ka nuna ‘yan ta’adda na sulalowa su na dawowa ciki.

Matasan da kan gudanar da ‘yan kananan harkokin kasuwanci da kuma ‘yan ayyukan samun kudin shiga; sun bayyana yanda su ke fatan yankin zai tsira daga miyagun iri da kuma ‘yan korafe-korafe kan yanda yanayin ya takura wa harkokinsu na yau da kullum.

ILIMI GARKUWAN DAN ADAM F 10 24 22.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:56 0:00

XS
SM
MD
LG