Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Ta Yi Kasafin Kudi Har Na Dala Biliyan Biyar


Sabon shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa baya da aka rantsar da shi
Sabon shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa baya da aka rantsar da shi

Kasar Zimbabwe ta samar da kasafin kudin shekarar 2018 da yakai har dalar Amurka Biliyan 5, tace kuma zata tabbatar ta yi dokar da zai janyo masu saka hannu jari.

Sabuwar gwamnatin Zimbabwe ta samar da kasafin kudi na shekara mai zuwa, har na dalar Amurka biliyan biyar.

Ana sa ran kasafin kudin zai farfado da tattalin arziki kasar da ke cikin wani mawuyacin hali.

Sai dai samun nasarar hakan sai idan har gwamnatin kasar za ta yaki cin hanci da rashawa, kana ta samar da zabe na gari.

Sanna ta samar da dokokin saka hannun jari da ke da walwala.

Wakilin Muryar Amurka a Zimbabwe, Sebastian Mhofu, ya ce a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin, Ministan kudi na kasar Patrick Chinamasa ya ce farfado da tattalin arziki kasar da ke ciki mawuyacin hali ba abu ne mai sauki ba .

Amma ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

Ya ce tilas ne gwamnati ta dauki matakan dawo wa ‘yan kasar da kwarin gwiwa akan harkokin kudin kasar da ma duk wani abu da ke da nasaba da batun kudi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG