Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Tana Shirin Gudanar Da Zabe A Cikin Watan Yuli


Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa

Zimbabwe zata gudanar da zabe a ranar 30 ga watan Yuli, karon farko da kasar da take kudancin Afrika zata yi zaben bayan lokacin da sojoji suka yi waje da shugabanta Robert Mugabe a watan Nuwamban bara.

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ne ya ajiye ranar 30 ga watan Yuli ta zama ranar zaben shugaban kasa da na wakilan majalisar kasa da kuma na zaben kansiloli.

Manangagwa mai shekaru 75 da haifuwa wanda kuma ya taba zama mataimakin shugaba Mugabe, shine zai jagorancin jami'iya mai mulki ta ZANU-PF ta fafata da babban jami'iyar adawa ta Movement for Democratic Change, wanda Nelson Chamisa mai shekaru 40 da haifuwa ke jagoranta. Shugaba Mnangagwa yayi alkawarin cewa za a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kuma ya mika gayyata ga masu sa ido daga kasashen waje su zo su duba yanda za a gudanar da zaben.

Wannan ne karon farko da Zimbabwe zata yi zaben da babu sunan Mugabe mai shekaru 94 a kan takardan zabe, tun bayan da kasar ta samu yancin kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG