Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zirin Gaza Na Dab Da Wargajewa-Mladenov


Jami'an tsaron Majalisar Dinkin Duniya
Jami'an tsaron Majalisar Dinkin Duniya

Nikolay Mladenov wakilin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da Gabas ta Tsakiya ya yi kashedin cewa Zirin Gaza na dab da wargajewa sanadiyar rikin Falesdinawa da Israilawa akan iyakarsu idan ba'a dauki matakan gagagawa ba

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya akan shirin samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya Nikolay Mladenov yayi kashedi jiya Laraba cewa Zirin Gaza yana dab da wargajewa, a saboda haka yayi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan ganin fada bai barke a yankin ba. Mr Mladenov yace tilas a dauki matakan gaggawa na hana barkewar wani yaki da kuma kawar da wahalar da mutane ke sha a yankin, sa'anan kuma a karfafawa gwamnatin Palasdina gwuiwa ta yi abinda ya kamata.

Nikolay Mladenov yayi wannan furucin ne wajen wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi akan wannan batu.

Yankin Palasdinawa yayi fama da tarzoma cikin yan makonin da suka shige a yayinda dubban Palsdinawa suka dinga yin zanga zanga duk ranar juma'a a katangar kan iyakar data raba Gaza da Isira'ila.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Palasdinawa saba'in da shidda ciki harda yara goma sha daya jami'an tsaron Isira'ila suka kashe, kuma fiye da mutane dubu uku suka ji rauni cikin wata daya.

Kwamitin sulhu yana tattauna wani daftarin kuduri da kasar Kuwait ta gabatar da ya bukaci a tura wata rundunar soji zuwa yankunan Pakasdinawa domin kare fararen hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG